Yadda bayanin yake ga 'yan uwa wadanda basu samu damar sanin bayanin da CBN tayi ba

 HATTARA




Yadda bayanin yake ga 'yan uwa wadanda basu samu damar sanin bayanin da CBN tayi ba.https://elmusteey.blogspot.com/2022/12/yadda-bayanin-yake-ga-yan-uwa-wadanda.html



▶ Za'a fara amfani da sababbin kudaden Naira 200, 500 da Naira 1,000 ranar *Al-Hamis 15 ga watan December 2022* din nan in sha Allah.


▶ Daga wannan ranar sababbin kudaden da tsofaffin duk za suyi ta aiki a matsayin Legal Tender, wato kudi na zahiri na gaskiya.


▶ Amma, daga ranar *31 ga watan January na shekara me zuwa, 2023* wadancan tsofaffin 200, 500 da 1,000 zasu *daina aiki* a hukumance.


▶ Abin nufi idan kaje ka kai kudin ranar *31 ga watan January* Banki, zasu karba ranar karshe kenan, washegari ranar *1 ga watan February (Watan Biyu) na 2023* idan kaje da kudin Banki ba zasu karba ba.


▶ Kuma kai ma kada ka kar6i tsofaffin kudaden a shagon ka ko wajen kasuwancin ka daga ranar *1 ga watan February,* domin ko kaje Banki *ba zasu karba ba.*


▶ Domin ka saukakawa kanka a wajen sana'ar ka, toh *ka daina kar6ar tsofaffin kudi daga ranar 25 ko 27 ga watan January kawai.*


▶ Duk Wanda zai baka ya baka daga cikin sababbi, domin akwai su a lokacin, suna nan suna zagayawa tare da tsofaffin.

Kada kaje kayi ta tara kudi da nufin zaka kai Banki wani dalili ya taso ya hana kaiwa, har a wuce 31 January, *idan kaje musu da kudin on 1 February ba zasu ko saurare ka ba ma.*


▶ Hatta masu POS suyi hankali, *su lura wajen karban kudade a yanzu da kuma lokacin da ake daf da 31 January, domin "Fake Notes" zasu iya shigowa cikin mutane,* idan baka saba ta'ammuli da kudi ba, ba zaka ta6a iya gane su ba, sai kaje Banki kaga ana ta ware maka su, ana cewa ba kudi bane.

 Takarda ce kawai ko plain sheet ne kawai yasha ado da penti kamar kudin gaske, alhali kai kuma an baka ka tura wa mutum ta Account, Transfer, kaga an barka da asara.

Allah ya tsare ya kiyaye!  

Amma gaskiya a lura da kudade sosai a 'yan wadannan watannin da suka rage.

Allah yasa mu dace! 


▶ Shawarata Agareku, kowa da kowa yaje *ya bude e-Naira wallet* tun yanzu. 

  Saboda dukkan hasashe ya nuna idan lokacin yayi za suce *kowa sai ya bude wallet na e-Naira* ya fara amfani da ita.  

*Kaje ka nemi masana subude maka wallet na e-Naira tunkafin gwamnati tafito tace kowa dole sai yayi amfani da ita* gwanda kayi tun yanzu, kar a zo ana yin rubibi abun ya zama da wahala. 

Idan ba kasan waye zai bude maka ba, ka shiga Telegram idan kana yi, 

ka rubuta:

*e-Naira community*

Za kaga Group kayi *Join* , kayi tambaya su taimaka maka ka bude *Wallet na e-Naira.* 

Allah yasa mu dace! 


*Dan Allah, a tura wannan saqon kowane Group na WhatsApps da Facebook dan ka taimaki al'ummar mu.*

Nagode

Comments

Popular posts from this blog

NG-CARE KADUNA STATE