GA ABUBUWAN DA ZAKA DUBA A WAYARKA IDAN KANA CRYPTO.
GA ABUBUWAN DA ZAKA DUBA A WAYARKA IDAN KANA CRYPTO.
A matsayin ka na Dan crypto wanda
muke kyautata zaton yana yawan amfani da waya, sau da yawa kana samun wadannan matsalolin:
https://elmusteey.blogspot.com/2022/12/ga-abubuwan-da-zaka-duba-wayarka-idan.html
1. Kana amfani da wayarka tayi ta slow ko kamewa lokacin sa ka shiga exchanger kana so kayi faka-faka kayi trading.
2. Idan zakayi verification na exchanger da zarar an turo OTP kayi minimizing ka duba, kana dawowa sai kaga app din ya dawo baya.
3. Wani lokacin sai ka shiga app kaga ya rubuta "App Stop" ya fito da kansa, wannan shi ake cewa crash.
Akasari idan masu siyan wayar android sunje siyan waya, suna tambayar kawai RAM dinta ne da Space "ROM". Amma kuma ba wannan ne kadai abin dubawar ba. Abu mafi mahimmaci a jikin waya shine "Processor" dinta. Bari na fada maka duk yadda ukun suke amfani.
1. RAM:- Idan kana amfani da wayarka dai kayi minimizing ka koma wani app din, kana dawowa sai kaga ya dawo baya. Toh wannan laifin RAM dinka ne karami.
2. PROCESSOR:- Idan kana amfani da wayarka sai kaga tana ta tafiya very slow sannan tana daukar zafi, to wannan kuma processor din wayarka ne karami.
3. Idan App suna yawan lalacewa a wayarka, wataran idan ka shiga sai kaga yaqiyi, to wannan matsalar memory din wayarka ne ROM, wayarka ba space.
Ga yadda ake gane girman RAM, PROCESSOR, ROM.
Akasari wayoyin da muke amfani dasu kowacce da kalar PROCESSOR din da kamfanunuwan suke amfani dashi bana kamfani daya bane. Saboda haka bari mu dauki kalar wayoyin da muka fi amfani dasu muyi bayani akan su.
Misalin Processor:
(I) PROCESSOR
1. INFINIX, TECNO, REDMI nasan sune wayoyin da aka fi amfani dasu a arewacin Nigeria. Suna amfani da wani processor da ake cewa "Helio G" wanda yanzu wanda yafi kowanne a cikin su shine "Helio G99".
2. NOKIA, SAMSUNG, HUAWEI, REDMI suna amfani wani lokacin da wani processor da ake cewa "Snapdragon", yanzu a jerin processor din daya fi kowanne na kamfanin snapdragon shine "Snapdragon 8 Gen 2"
3. SAMSUNG suna amfani da wani processor mai suna "Exynos" akasari Samsung sunfi amfani dashi fiye da kowanne processor, sannan babban ciki shine "Exynos 990"
4. IPHONE kuma suna amfani da wani processor me mai suna "A Bionic", sannan duk waya suna chanza shi, yanzu babban ciki shine "A14 Bionic".
(II) RAM
Shi kuma numbobi ne kawai, amma shi kuma yana farawa daga 2GB RAM, har zuwa inda Allah yakai mai rai.🙃
(III) ROM
Shima iya kudin ka, iya shagalinka. Yana farawa tun daga 16GB har zuwa 1T, amma akasari wayoyin android suna tikewa ne a 256GB.
"Saboda haka a kula sosai, Processor shine yafi komai amfani a jikin waya fiye da sauran abubuwa da muke damuwa dasu, zakaje siyan waya ayita maka over hyping din RAM da space dinta, ka duba processor dinta"
Ga misalin hoto nan na ajiye( Processor "Helio G99". RAM "13GB", Space "256GB")
BISSALAM
IBN ELMUSTAPHER BUSINESS ENTERPRISES

Comments
Post a Comment